Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labaran Wasanni

Yan wasan Brazil 8 a Firimiyar Ingila ba za su buga wasan karshen makon nan ba

Published

on

Biyo bayan dakatar da wasan neman tikitin buga gasar cin kofin Duniya tsakanin Brazil da Argentina a kalla ‘yan wasan kasar Brazil 8 dake buga gasar Firimiyar kasar Ingila ne ba za su buga gasar ba a karshen makon da muke ciki.

Hakan ya biyo dokar da hukumar kwallon kafar Ingila ta saka na hana duk wani Dan wasan dake wasa a kasar buga wasa na tsawon mako 2 sakamon killace kanshi da zai.

Hukumar kwallon kafa ta Brazil ta dakatar da shugaba Rogerio Caboclo

Hukumar kwallon kafa ta Duniya FIFA ce dai ta saka dokar ta hana duk wani Dan wasa shiga cikin ‘yan uwanshi na tsawon mako 2.

Dakatar da ‘yan wasan dai zai shafi kungiyar kwallon kafa ta Liverpool, Manchester City, Chelsea, Manchester United da kuma Leeds United.

Kasar Brazil dai ta saka dokar Hana ‘yan wasan kasar Ingila shiga kasar sakamakon saka kasar da ta yi cikin kasashe masu hatsarin dangane da annobar Corona.

Hakan ne yasa aka dakatar da wasan kasar ta Brazil da kasar Argentina na neman tikitin buga gasar cin kofin Duniya da za’a gudanar a kasar Qatar a shekarar 2022.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!