Kiwon Lafiya
Filato:Kimanin sama da kaji dubu dari uku ne suka mutu sanadiyar murar tsuntsaye
Sama da kaji dubu uku da dari tara ne suka mutu sakamakon kamuwa da cutar murarar tsuntsaye wadda ta bula a jihar filato a baya-bayan nan.
Babban jami’in asibitin kula da dabbobi ta kasa da ke jihar filato Dr. Spak Shaset ne ya bayyana haka ga manema labarai jiya a garin Jos.
Ya ce annobar murar tsuntsayen ta shafi wasu manyan gidajen gona guda biyu a garin Jos.
Haka kuma ya ce, ko a watan Janairun da ta gabata ma an samu irin wannan annobar murar tsuntsayen a wasu sassa na jihar Bauchi.
Dr. Spak Shaset, ya ce bayan sun dauki samfarin kwayar cutar a matakin gwaji sun tababatar da cewa cutar murar tsuntsaye ce, kuma kawo yanzu tuni suka dauki matakin gaggawa domin dakile cutar don gudun kamuwar wasu gidajen gona a yankin.
Haka zalika ya shawarci masu kiwon dabbobi a jihar ta Filato da su kula da dabbobinsu ta hanyar basu kulawar da ta kamata tare da kai rahoton irin wannan cutar.