Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Kiwon Lafiya

Annobar Amai da Gudawa tayi sanadiyyar mutuwar mutane 37 a jihar Jigawa

Published

on

Babban Sakatare a ma’aikatar lafiya a jihar jigawa yace sama da mutane Talatin da Bakwai ne suka rasa rayukansu a dalilin bullar cutar amai da gudawa a wasu kananan hukumomin jihar.

Dakta Salisu Mu’azu, ya kuma ce yanzu haka akwai mutane dubu biyu da suka kwance a Asibitoci suna samu kulawa dalilin kamuwa da cutar.

Ya ce kananan hukumomin jihar tara abin ya shafa, sai dai cutar tafi kamari a kananan hukumomin Hadeja da Dutse da kirikasamma da Birnin Kudu da kuma Ringim.

Babban sakatren ya ce kusan wata biyu kenan da fara bullar cutar a jihar, kuma gwamnatin na kokarin ganin an kawo karshen annobar da ta addabi wasu kananan hukumomin jihar.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!