Connect with us

Labarai

Gambari ya gana da kwamitin binciken Magu

Published

on

Shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa Farfesa Ibrahim Gambari ya yi wata ganawa ta musamman da ‘yan kwamitin shugaban kasa da ke bincikar zargin dakataccen shugaban hukumar EFCC Ibrahim Magu da aikata almundahana.

Rahotanni sun ce babu karin haske kan batutuwan da suka tattauna, sai dai ana ganin hakan baya rasa nasaba da batun binciken da suke yi kan Ibrahim Magu.

A jiya talata ne dai rahotonni suka bayyana cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ya dakatar da Ibrahim Magu daga mukaminsa na shugabancin hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta EFCC.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a Reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Archives

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!