Labarai
Fiye da dalibai miliyan 2 ne suka cinye sama da darusa 5 a WAEC
Hukumar gudanar da jarabawar kasashen Afirika ta yamma ta bayyana cewar dalibai 1,287,920 ne suka samu kredit a darussa biyar daga sakamakon jarabawar kammala sakandare ta yammacin Afirka (WASSCE) da aka gudanar tsakanin 8 ga watan Mayu zuwa Yuni na wannan shekara.
Jaridar LEADERSHIP ta bayyana cewar hukumar jarabawar cewa dalibai 1, 621, 884 ne suka yi wa WASSCE rajista daga makarantun sakandire 20,867 da aka tantance.
Daga cikin dalibai 1,613, 733, da suka zana jarabawar 1,361, 608 da ke wakiltar kashi 84.83 cikin dari sun samu kiredit biyar a cikin darussan da suka rubuta a jarabawar
Hakanan, dalibai 1, 287, 920 sun sami kiredit biyar da suka hada da Lissafi da Ingilishi. Wannan shine kashi 79.81 na jimlar daliban.
A cikin 2022, adadin dalibai da suka sami maki biyar sun kasance kashi 76.35 cikin dari ciki har da Lissafi da Ingilishi. Wannan yana nufin an sami raguwar aikin kashi 3.45 cikin ɗari.
Dalibai 262,803 da ke wakiltar kashi 16.29 cikin 100 na daliban da suka zana jarrabawar, ana hana su ne sakamakon rashin gudanar da jarabawar kokuma laifin satar amsa.
Hukumar ta bayyana cewar duk wani dalibi da aka samu yana satar amsa ta kowace hanya za’a tabbatar da cewar an soke masa sakamakon jarabawarsa ba tareda tazo hannunsa ko kuma makarantar da ya rubuta ba.
You must be logged in to post a comment Login