Kiwon Lafiya
Fiye da ma’aikatan jihar Kano 3,000 ne su ka yi rijista da hukumar taimakekeniyar lafiya
Gwamnatin Jihar kano ta ce, ya zuwa yanzu sama da ma’aikatan gwamnati dubu 3 ne su ka yi rijista da hukumar taimakekeniyar lafiya ta jihar.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na ma’aikatar lafiya ta jihar Isma’il Garba Gwammaja ya fitar, tana mai cewa sama da cibiyoyin kiwon lafiya 200 su ma sun shiga cikin tsarin.
Sanarwar ta kuma ce kwamitin ya ziyarci fiye da kananan hukumomi 13 tare da raba kayayyakin aiki sama da 215 ga cibiyoyin kiwon lafiya daban-daban na jihar.
Haka haka kuma sanarwar ta ruwaito kwamishinan lafiya na jihar Kano Dr Kabiru Ibrahim Getso, yayin wani taro da hukumar raya kasashe ta Burtaniya da ya gudana a jihar Kaduna, ya na shawartar ma’aikatan lafiya da su cigaba da tallata tsarin domin kowa ya shiga ciki.
Sanarwar ta kuma ce shugaban hukumar inshorar lafiya ta jihar Katsina Abdullahi Sani Gwarzo da farfesa Bala Kofar mata da wasu masu ruwa da tsaki sun gabatar da Makalu yayin taron.