Ƙetare
Fiye da mutane 1,500 ne suka rasa muhallansu a Sudan bisa tabarbarewar tsaro- IOM

Hukumar Kula da ‘yan gudun hijira ta Duniya IOM ta sanar cewa mutane 1,205 ne suka rasa matsugunansu daga biranen Bara da Umm Ruwaba a jihar Kordofan ta Arewa, yayin da wasu 360 suka rasa matsugunansu a Al-Abbasiya da Delami a Kudancin Kordofan saboda taɓarɓarewar tsaro.
A wata sanarwa da ta fitar IOM ta ce, ƙungiyoyinta da ke aiki a ƙarƙashin shirin tantance adadin yawan ‘yan gudun hijira wato ‘Displacement Tracking Matrix program, sun ƙiyasta cewa daga cikin waɗanda suka rasa matsugunansu daga Arewacin Kordofan, 580 sun tsere daga Bara, yayin da 625 suka bar Umm Ruwaba.
Sanarwar ta kara da cewa ‘yan gudun hijirar sun bazu a wurare daban-daban a Arewacin Kordofan da kuma wasu garuruwa da dama a jihar White Nile da ke kudancin Sudan.
You must be logged in to post a comment Login