Labaran Wasanni
Freedom Radio za ta buga wasan sada zumunci da Guarantee Radio

Freedom Radio za ta buga wasan sada zumunci da Guarantee RadioKungiyar kwallon kafa ta Freedom Radio za ta karbi bakuncin takwarar ta Guarantee Radio a wasan sada zumunci.
An shirya wasan ne don murnar bikin auren shugaban sashen shirye-shirye na Guarantee Radio Suyudi Isa Jibril Bichi.
Wasan zai gudana a ranar juma’a da karfe hudu na yamma a filin wasa na Freedom Arena dake harabar gidan Radio Freedom.