Connect with us

Labaran Wasanni

French Open 2020: Diego Schwartzman ya doke Dominic Thiem

Published

on

Diego Schwartzman ya yi nasarar doke Dominic Thiem a wasan daf da na kusa da na karshe a gasar French Open.

Sun dai shafe sa’anni biyar su na fafatawa a filin wasa na Roland Garros.

Thiem ya ce “Daga karshe na yi duk iya bakin kokarina. Lallai akwai abun al’ajabi a wasan na tsawon sa’anni biyar domin wannan shi ne na farko a tarihin wasanni na.”   

“Wannan nasarar na da matukar muhimmanci a gare ni. A zagaye na biyu da na uku, na shiga rudani har na dinga zargin kai na saboda na samu damammaki da yawa, lallai ya kamata na yi nasarar cinye wasan” a cewar Schwartzman.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 334,784 other subscribers.

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!