Labarai
Fulani da dama sun jikkata sakamakon harin da aka kai musu a Bukuru
Mutane da dama daga cikin Fulani sun jikkata sakamakon wani hari da aka kai musu a Bukuru, da ke Jihar Plateau, yayin da suke dawowa daga Kasuwar Dabbobi.
Kwamishinan Yaɗa Labarai da Sadarwa na jihar, Joyce Lohya Ramnap, ta tabbatar da harin a wata sanarwa da ta fitar a jiya litinin.
Gwamnatin jihar ta yi Allah wadai da lamarin tare da jajanta wa iyalan waɗanda abin ya shafa, yayin da jami’an tsaro ke gudanar da bincike domin gano waɗanda suka kai harin.
Gwamnatin Plateau ta kuma yi kira ga al’umma, ’yan kasuwa da makiyaya da su kwantar da hankula, tare da guje wa ramuwar gayya da ɗaukar doka a hannunsu. Ta ce tana tattaunawa da masu ruwa da tsaki domin ƙarfafa tsaro a hanyoyin da ake ganin suna da haɗari da kuma hana sake faruwar irin waɗannan hare-hare.
You must be logged in to post a comment Login