Labarai
Ƙungiyar SSANU ta bai wa Gwamnatin Tarayya wa’adin makonni 2
Ƙungiyar Manyan Ma’aikatan Jami’o’i ta Kasa SSANU, ta bai wa Gwamnatin Tarayya wa’adin kwanaki 14 da ta biya bashin albashin da suke binta ko su tsunduma yajin aiki.
Shugaban ƙungiyar na ƙasa, Mohammed Ibrahim, ya ce idan gwamnati ta gaza biyan bashin cikin wa’adin, ƙungiyar za ta shiga yajin aikin gama-gari ba tare da wani ƙarin sanarwa ba.
Ya ce bashin ya haɗa da na albashin da ya taso daga sabon tsarin albashin CONTTA, wanda ya fara aiki daga ranar 1 ga Janairu, 2026, da kuma albashin watanni biyu da aka riƙe wa ma’aikata a lokacin yajin aikin shekarar 2022.
Kungiyar ta SSANU ta kuma nemi a biya ma’aikatan bashin ƙarin albashin kashi 25 da 35 cikin ɗari na tsawon shekara guda.
Haka zalika kungiyar ta yi kira ga gwamnati da jami’o’i da su samar da isassun kuɗaɗen gudanar da jami’o’i, musamman bangaren lantarki, dakunan gwaje-gwaje, ɗakunan karatu da tsaro.
You must be logged in to post a comment Login