Labarai
Kashim Shettima ya tafi Habasha domin halartar taro

Mataimakin shugaban Najeriya Sanata Kashim Shettima, ya yi balaguro zuwa ƙasar Habasha domin halartar taron gwamnatocin ƙasashen biyu kan bunkasa abinci mai gina jiki.
Wannan na kunshe cikin sanarwar da mataimaki na musamman kan harkokin yada labaran sa Mr Stanley Nkwocha ya fitar a yau, da ya ce Shettima na halartar taron ne ƙarkashin goron gayyatar mataimakin Firai Ministan kasar Habasha, Temesgen Tiruneh.
Haka kuma mataimakin shugaban Najeriyar zai gana da masu ruwa da tsaki a fannin cimaka da kaddamar da shirin tsakanin kasar da Habasha.
Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da ake nuna damuwa kan tasirin sauyin yanayi kan amfanin gona, da a wasu lokutan ake samun jinkirin girbi da rashin kyawun yabanya.
You must be logged in to post a comment Login