Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Sama da mutum 11,000 sun warke daga Corona cikin kwana guda a Najeriya

Published

on

Masu cutar Corona 11,188 ne suka warke daga cutar Corona a jiya Laraba, kamar yadda cibiyar dakile cutuka masu yaduwa ta kasa NCDC ta sanar.

A sanarwar da NCDC ta fitar a ranar Litinin da ta gabata, ta ce mutane 20,663 ne suka warke daga cutar a fadin kasarnan.

Sai dai a jiya Talata an samu ci gaba, inda NCDC ta ce adadin wadanda suka warke ya kai 31,851 wanda hakan ke nufin mutum 11,188 sun warke a rana daya.

Wannan shi ne adadi mafi yawa na wadanda suka warke daga cutar a rana guda, tun bayan bullarta a Najeriya.

NCDC ta kara da cewar mutum 910 ne Covid-19 ta yi ajalinsu a sassan Najeriya.

Adadin wadanda suka kamu da cutar a Najeriya zuwa yanzu ya kai 44,433.

Sai dai a yanzu mutum 11,627 suka rage wadanda ke jiyyar cutar a sassan kasarnan, kamar yadda NCDC ta sanar a daren Talata ta babban shafinta na internet.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!