Labaran Kano
Gado na neman raba kan ‘yan uwa
Wani magidanci mai suna Malam Sagir Dorayi, ya shigar da karar dan uwansa da yake da’awar cewa sun hada uwa amma uba kowa da na shi.
Sagir Dorayi ya gurfanar da shi ne a gaban kotun shari’ar musulunci da ke Kofar Kudu yana mai neman kotun ta raba musu gadon da mahaifin su Malam Ali Ahmad ya rasu ya bari a ‘yan kwanakin da suka gabata.
A zaman kotun na jiya Laraba, Sagir Dorayi ya bayyana wa Alkalin kotun Malam Ibrahim Sarki Yola cewa, wanda yake karar ya yi da’awar cewa ya san mahaifiyarsu daya amma bai amince mahaifinsu daya ba.
Sai dai a zaman kotun lauyan wanda aka yi kara Barista Ibrahim Mu’azzam ya shaida wa kotun cewa shi ne yake kare magadan wadanda suka hadar da Allhaji Kabiru Ali Ahamad da Binta Cima Ali Ahmad da kuma Nasir Ali Ahmad, inda ya kara da cewa, dukkan wadanda yake karewar ba su amince mahaifinsu daya da mai karar ba.
Da yake suka bisa da’awar wadanda ake karar, lauyan mai kara Barista Ibrahim Abdullahi Chedi, ya musanta da’awar tasu inda nan take ya bukaci a bashi damar yiwa mahaifiyar su tambayoyi.
Nan take Alkalin ya amince da bukatar mai kara na ayi wa mahifiyar su tambayoyi.
Da take amsa tambayoyin, mahaifiyar tasu Hajiya Amina ta shaida wa kotun cewa Sagiru da Kabirun dukkan su ‘ya’yan ta ne kuma marigayi Malam Ali Ahmad mazaunin unguwar Nassarawa GRA shi ne mahaifinsu, baki daya, kuma lokacin da take haihuwa ta kan yi shi ne Akufi-Akufi a don haka ya shay a bashi ne.
Kotun dai ta dage cigaba da sauraron karar zuwa ranar 18 ga wannan wata da muke ciki na Oktoba domin cigaba da sauraron karar.