Labarai
Gamayyar kungiyar hadin kan Arewa ta baiwa yan kabilar Igbo wa’adin barin yankin Arewa
Gamayyar kungiyar hadin kan Arewa da ta taba baiwa ‘yan-kabilar Igbo wa’adin barin yankin Arewa a bara, ta nuna rashin amincewarta kan matsayar da gwamnonin Arewa da ma Jam’iyyar APC suka dauka dangane da sake fasalin kasa.
Sanarwar hakan na kunshe ne cikin jawabin bayan taro da mai magana da yawun kungiyar ta The Coalation of Northern Group Abdul’aziz Sulaiman ya karantawa manema labarai jiya a Kaduna.
Sanarwar ta ci gaba da cewa jiga-jigan siyasar Arewa na dab da tafka gagarumin kuskure matukar da amince da wannan kuduri da bai yi daidai da bukatar mafi-akasarin al’umma ba, wanda hakan ka iya jefa yankin cikin halin rashin tabbas.
Kungiyar ta ce hakika yankin Arewa yana goyon bayan yunkurin sake fasalin kasa kuma a shirye suke domin shiga muhawara ta ko wane fanni domin kare muradun Arewa matukar za a yi hakan ba tare da nun fifiko ba.
Haka zalika kungiyar ta bukaci a sake sabon tsari na wakilci da zai kunsi kowa-da-kowa, sannan ta ce ba ta goyon bayan tura wadanda shekarunsu suka haura 70 zuwa taron tattauna makomar kasa.