Labarai
Ganduje : Ana cigaba da raba maganin zazzabin cizon sauro
Daga Shamsiyya Farouk Bello
Yayin da ake ci gaba da gangamin aikin rarraba maganin rigakafin zazzabin cizon Sauro anan jihar Kano, a unguwar Tukuntawa dake yankin karamar hukumar birnin Kano, sun bayyana cewa maganin rigakafin ya samu karbuwa tsakanin al’ummar yankin.
Sai dai kuma sun ce, a wasu wuraren ana samun tasgaro, inda wasu suke kin karbar maganin rigakafin.
Shelar da wasu daga cikin ma’aikatan da ke aikin rarraba maganin zazzabin cizon sauro a nan Kano Kenan ya sanya mutane farga wajen ana rabon
A yayin zagayen gani da ido da gidan Radio Freedom ya Gudanar a cikin unguwar ta Tukuntawa dake karamar hukumar birnin Kano, ta riske gidaje da dama sun karbi wannan rigakafi.
Haka zalika gidan Radio Freedom din ya riske ma’aikata na rabon wannan maganin rigakafin cutar zazzabin cizon Sauron, wadanda suka ce maganin ya samu karbuwa sosai a wurin al’umma.
Duk da cewa akwai inda sukaci karo da matsala, inda suka kai maganin wani gida, bayan sun fito akasa yara suka zubar a kwata, wanda hakan ya nuna anada bukatar kara wayar da kan jama’a dangane da mahimmancin magani ga lafiyar al’umma.
Wakiliyarmu Shamsiyya Farouk Bello na da ta tattaro ra’ayoyin mutane ta rawaito cewa, daya daga cikin ma’aikatan da suke rabon wannan maganin rigakafin ya ce mutane sun fito don karbar riga kafin
Wkiliyar Radio Freedom ta rawaito cewa , duk da karbuwar da wannan maganin ya samu a cikin al’umma, wayar da kan al’umma na da mahimmanci, dangane da mahimmancin wannan rigakafi ga lafiyar al’umma.
You must be logged in to post a comment Login