Labarai
Ganduje: Babu tabbacin ko za mu iya biyan dubu 30,600 ga ma’aikata a watan Afrilu
Gwamnatin jihar Kano ta ce babu tabbacin ko za ta biya mafi karancin albashi na naira dubu talatin da dari shida ga ma’aikatan jihar a wannan wata na Afirilu.
Gwamnan Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje wanda kwamishinan yada labarai na jihar Kano kwamared Muhammed Garba ya wakilta, shine ya bayyana haka yayin zantawa da manema labarai, bayan kammala taron da kungiyar kwadago ta kasa (NLC) ta shirya a ranar juma’a a Kano.
Sai dai ya ce har yanzu gwamnatin Kano ba ta sauya matsaya ba kan biyan naira dubu talatin da dari shida ga ma’aikata a matsayin mafi karancin albashi, amma hakan ya danganta ne kawai ga yadda ta samu kasonta na rabon arzikin kasa daga asusun tarayya.
A nasa bangaren shugaban kungiyar kwadago ta kasa (NLC) reshen jihar Kano kwamared Kabiru Ado Munjibir, ya ce, gwamnati ta yi musu alkawarin biyan dubu talatin da dari shida idan aka samu isassun kudade daga asusun tarayya.
Ya kuma ce kungiyar za ta ci gaba da gwagwarmaya don kare muradun ma’aikatan jihar.
You must be logged in to post a comment Login