Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labaran Kano

Ganduje da Sarkin Kano sun gana da masu zuba jari daga kasar China

Published

on

Gwamnan Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya tattauna da wakilan masu zuba jari daga kasar China wajen fito da hanyoyin zuba jari tsakanin jihar nan da yankin Shandong dake China.

Wannan na kunshe ne cikin wata sanarwa da sakataren yada labaran Gwamnan Kano Abba Anwar ya sanyawa hannu a yau, jim kadan bayan wani taron hadaka da Gwamnan ya jagoranta da Sarkin Kano Muhammadu Sanusi na biyu a wani bangare na tattauna hanyoyin da jihar nan ka iya amfana daga masu zuba jarin daga kasar China.

Gwamna Ganduje ta cikin sanarwar ya ce ya zama wajibi su maida hankali kan bangarorin masana’antun masaku da fatu da Noman Alkama da shinkafa da kuma ma’adanai, wanda a cewar sa hakan zai amfanar da jihar Kano da masu zuba jari daga yankin Shandong na kasar China.

Taron dai ya gudana a jihar Lagos, a matsayin bibiyar ziyarar da sarkin Kano ya kai kasar ta China a baya-bayan nan tare da wakilai daga bangaren Gwamnatin Kano karkashin jagorancin mataimakin Gwamnan Dr. Nasiru Yusuf Gawuna.

Hoto a yayin zaman tattaunawar

Ganduje ya kuma kara da cewa, shakka babu wannan alaka za ta amfanar da duka bangaorin biyu, duba da yawan al’ummar da Allah ya buwacewa jihar Kano.

Ya ce kasancewar kowane mai zuba jari, na nemar inda zai samu kasuwa ne ya sanya Kano ta zama mafi dacewar wurin da ya kamata a zuba jari.

Ya kuma bayyana cewa sanya mai martaba sarkin Kano ya jagoranci kwamitin, an yi shine da kyakkyawar manufar cimma nasara, duba da kwarewar sa a bangaren tattalin arzikin kasa.

Ganduje ya kuma bukaci shugaban masu zuba jarin da ya mayar da hankali wajen duba yanayin da ilmi ke ciki a jihar Kano, don cika bangaren yarjejeniyar da suka sanya hannu da su.

Rubutu mai nasaba:

Sarki Muhammadu Sanusi II ya nada Sarkin Hausawan Turai

Sarkin Kano yace zai cigaba da kare mutuncin masarauta

Sakataren yada labaran Gwamnan Kanon Abba Anwar ta cikin sanarwar, ya ce sarkin Kano Muhammadu Sanusi na biyu ya bayyana godiyar sa ga masu zuba jarin na kasar China, inda ya tunasar da su kan cewa su duba hanyoyin makamashi da ya hada da na hasken rana a matsayin muhimman bangarori.

Hoto daga wurin tattaunawar

Cikin tawagar da suka halarci taron sun hadar da shugaban ma’aikatan fadar Gwamnan Kano Ali Haruna Makoda da Sarkin Shanun Kano Shehu Usman Muhammad da manajan daraktan hukumar dake kula da kadarorin jihar Kano Dakta Jibrila Muhammad, sai kuma babban daraktan sashen kasuwanci na ma’aikatar kasuwanci ta jihar Kano Abdullahi Idris.

Yayin da daga bangaren masu zuba jarin na kasar China akwai Mista Liu Yongju da sakatare janar na masu zuba jarin na Shandong Mista Zhang Xigcheng.

Sauran sun hadar da wani kwararre Mista Zhao Qing da sauran wakilai.

Sanarwar ta kuma kara da cewa, wakilan masu zuba jarin na kasar China za su kasance a jihar nan gobe Alhamis don tattaunawa wajen fara aiwatar da yarjejeniyyar da suka kulla tsakanin su.

Rubutu masu nasaba:

Sarkin Kano ya bukaci masu rike da sarautun gargajiya su yi aiki kafada-da-kafada da hukumar ilimin manya

Sarkin Kano ya dakatar da mai Unguwar Badawa

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!