Connect with us

Kiwon Lafiya

Sarkin Kano ya bukaci masu rike da sarautun gargajiya su yi aiki kafada-da-kafada da hukumar ilimin manya

Published

on

Mai martaba Sarkin Kano Malam Muhammadu Sanusi II ya bukaci masu rike da sarautun gargajiya da su yi aiki kafada-da-kafada da hukumar bada ilimin manya da nufin samun ingantaccen ilimi a yankunan su.

Sarki Muhammadu Sanusi II na wannan umarnin ne a yayin da jami’an hukumar kula da ilimin manya ta jiha a karkashin jagoranci babban Darakta, Abdulmumin Liman Yusuf, suka kai masa ziyara a fadar sa.

Sarkin ya bayyana cewa akwai bukatar hukumomin ilimi su farfado da rubutun karatun ajami da nufin inganta ilimin ajamiwanda magabata sukai amfani dashi tun farko wajan cimma burinsu na rayuwa kafin shigowar ilimin nasara a kasashen Hausa.

Tun farko da yake jawabi, Babban daraktan Hukumar Abdulmumin Liman yace sun zo fada ne da nufin sanarwa da sarki irin ayyukan hukumar nailimantarwa da fadakarwa akan muhimmancin ilimi.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!