Labarai
Ganduje ne jagoran APC a Kano- Maimala Buni
Wannan bayani dai na ƙunshe a cikin wata wasiƙa da shugaban riƙon jam’iyyar APC Maimala Buni ya aike wa Gwamna Ganduje kamar yadda Kwamishinan yaɗa labaran Kano Malam Muhammad Garba ya wallafa a shafinsa na Facebook.
Wannan wasiƙa ta fara da yin waiwaye kan yadda rikicin cikin gidan ya somo, har zuwa ga batun tafiya kotu da kuma ƙalubalantar hukuncin kotu da ɓangaren Gwamnati ta yi.
Daga nan ne kuma sai Maimala Buni ya zayyano irin ƙoƙarin da suka yi na ganin an sulhunta an samu daidaito a tsakani.
APC ta ci gaba da cewa, bayan haka ne ya sanya ta ɗaukar manyan matakai guda huɗu.
- Mataki na farko shi ne sauke kowa daga muƙami tun daga matakin mazaɓu har zuwa jiha na jam’iyyar a nan Kano.
- Mataki na biyu jam’iyyar ta ce, Ahir ga wani ɗanta ya kuma tsoma baki a sabgar jam’iyyar a wata ƙaramar hukuma da ba tasa ba.
- Na uku jam’iyyar ta umarci a kafa kwamitin masu ruwa da tsaki a kowace ƙaramar hukuma domin samar da sabbin shugabanci.
- An kuma kafa Kwamiti na haɗin gwiwa tsakanin uwar jam’iyyar da kuma matakin jiha, wanda shi ne zai riƙa karɓar rahoton ƙananan hukumomi.
Wannan Kwamiti ya ƙunshi Gwamna Dr. Abdullahi Umar Ganduje a matsayin jagora, sai kuma Sanata Malam Ibrahim Shekarau, da tsohon shugaban majalisar wakilai Yakubu Dogara da Gwamnan jihar Zamfara Alhaji Bello Matawalle, sai kuma Sanata Abba Ali.
Baya ga wannan jam’iyyar ta yi wasu kalamai mai kama da dannar ƙirji domin kuwa a wata gaɓar ta bayyana cewa, Gwamna Ganduje shi ne jagoran jam’iyya, kuma ana ƙarfafarsa da yayi duk mai yiwuwa wajen haɗin kan masu ruwa da tsakinta.
Saboda haka ana fatan Gwamnan zai tabbatar da adalci da daidaito ga kowane ɓangare.
Maimala Buni ya kuma jaddada cewa, adalcin da yake magana bai tsaya iya ga rabon muƙaman jam’iyya ba, a’a ana fatan Gwamna ya ɗinke a koma uwa ɗaya uba ɗaya.
Jam’iyyar ta ce, ba mai yiwuwa bane, a ce kowane ɓangare sai ya samu abin da yake so ɗari cikin ɗari, amma abin da take buƙata shi ne a fifita maslahar jam’iyyar a gaba.
Da ta waiwaya kan batun kotu kuwa jam’iyyar ta yi takaici tana mai cewa, shari’a ba za ta haifar da ɗa mai ido ba, domin kowane ɓangare na buƙatar kowa.
You must be logged in to post a comment Login