Connect with us

Labarai

Ganduje ya aikewa majalisar dokoki sunayen mutum biyu – KANSIEC

Published

on

Gwamnan jihar Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje, ya aike wa majalisar dokoki ta jihar sunayen wasu mutane biyu domin tantance wa gabanin a nada su a matsayin kwamishinoni a hukumar zabe mai zaman kanta ta jihar Kano KANSIEC.

Shugaban majalisar dokokin ta jihar Kano Abdul’aziz Garba Gafasa ne ya karanta wasikar a zaman majalisar na yau Talata.

Mutanen biyu da gwamnan ya aike da sunayen nasu don tantancewa su zama kwamishinoni na biyu da na uku sun hadar da Aisha Abubakar Bichi da kuma Idris Haruna Gezawa.

Karin labarai:

Yadda zaman majalisar dokokin Kano ya kasance a yau

Majalisar dokokin Kano ta dawo daga hutu

Haka kuma wasikar da gwamnan ya aiko ta bukaci majalisar ta tantance Idris Garba Unguwar Rimi da za a nada a matsayin wakili a majalisar zartaswa ta jihar Kano.

Wakilin mu na majalisar dokokin ta jihar Kano Auwal Hassan Fagge, ya ruwaito cewa, a makon da ya gabata ne gwamnan ya aike wa majalisar sunan Malam Ahmad Rufa’i Yalwa don neman sahalewar su ya zama kwamishinan na daya a hukumar ta KANSIEC.

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Archives

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!