Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Majalisar dokoki ta bukaci Ganduje ya magance matsalar ruwa a Kano

Published

on

Majalisar dokoki ta jihar Kano ta bukaci gwamnatin jihar kan ta yi duk mai yiwuwa wajen shawo kan matsalar karancin ruwan famfo da ake fama da shi a wasu daga cikin sassan kananan hukumomin cikin birnin Kano guda 8.

Bukatar ta biyo bayan kudirin gaggawa na hadin gwiwa da wakilan kananan hukumomin suka gabatar ta hannun dan majalisa mai wakiltar karamar hukumar Dala a majalisar Lawan Usaini Chediyar ‘yan gurasa ya gabatar gaban zauren majalisar a zamanta na ranar Laraba.

Da yake gabatar da kudirin Lawan Usaini Chediyar ‘yan gurasa, ya ce, al’umnar kananan hukumomin na cikin birnin Kano da suka hadar da karamar Hukumar Birni da Dala da Gwale da Nassarawa da Fagge da Ungogo da Tarauni da kuma karamar hukumar Kumbotso, dukkansu suna fama da kamfar ruwa.

Haka kuma a zaman majalisar na yau, majalisar ta tan-tance Idris Garba Unguwar Rimi bayan da kwamitin kula da harkokin zabe na majalisar ya kammala bincike a kansa domin nada shi a matsayin kwamishina.

Karin labarai:

Kai tsaye: Hotunan yadda zaman majalisar zartarwa ta kasa ke gudana

Ganduje ya aikewa majalisar dokoki sunayen mutum biyu – KANSIEC

Da yake jawabi ga manema labarai na majalisar Idris Garba Unguwar Rimi, ya bayyana cewa zai yi duk mai yiwuwa wajen sauke nauyin da aka dora masa.

Wakilinmu na majalisar dokokin ta jihar Kano Auwal Hassan Fagge, ya ruwaito cewa, shugaban masu rinjaye na majalisar Kabiru Hassan Dashi ya jagoranci karatu na biyu na asusun taimake-keniya kan harkokin lafiya da gwamna Ganduje ya aike wa majalisar domin yi masa gyara.

Ya ce yin gyaran zai taimaka matuka wajen kawo gyara a asibitocin jihar Kano.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!