Labarai
Ganduje ya aike wa ‘yan asalin Kano mazauna Oyo tallafi
Gwamnatin jihar Kano ta aike da tallafin naira miliyan goma sha takwas ga mutanen da rikicin jihar Oyo ya shafa a makon da ya gabata.
Gwamnan jihar Dakta Abdullahi Umar Ganduje ne ya aike da talafin ga yan asalin jihar Kano wadanda rikicin kabilanci da ya shafa a kasuwar Sasa da ke Ibadan.
Kwamishinan yada labaran jihar Kwamared Muhammad Garba ne ya jagoranci tawagar kai tallafin, wanda kuma aka bai wa kowanne mutum guda naira dubu dari don rage musu radadi, kamar yadda ya yiwa freedom redio karin bayani.
ya ce, sun kai tallafin ga kimanin sama da mutum 180 yan asalin Kano mazauna jihar ta Oyo.
Cikin tawagar sun hadar da Kwamishinan harkokin kwasuwanci Barista Ibrahim Mukhtar da kwamshinan Ilimi Malam Muhammad Sunusi Kiru, wanda kuma gwamnan ya umarci da su ziyarci kowanne dan asalin jihar Kano da ke zaune a jihar ta Oyon don bashi tallafin.
You must be logged in to post a comment Login