Connect with us

Labarai

Ganduje ya baiwa sabon sarkin Rano takardar kama aiki

Published

on

Gwamnan jihar Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya baiwa sabon sarkin Rano maimartaba Alhaji Kabir Muhammad Inuwa takardar kamar aiki.

Maitaimakawa gwmanan Kano kan sabbin kafafan sadarwa na zamani Abubakar Aminu Ibrahim ne ya sanar da hakan ta shafinsa na Facebook kamar yadda kuke gani a kasa.

Kwanaki biyu da suka wuce ne, gwamnatin Kano ta sanar da nadinsa a matsayin sabon sarkin Rano, bayan rasuwar Sarkin Rano Alhaji Tafida Abubakar Ila Autan Bawo.

Karin labarai:

Yanzu-yanzu: Sarkin Rano ya rasu

Sarkin Rano ya dakatar da wasu Hakimai

A shekarar da ta gabata ne gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje ya amince da dokar kirkira sabbin masarautu hudu masu daraja ta daya a jihar wanda ya kai yanzu jihar tana da masarautu biyar.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Archives

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!