Labarai
Ganduje ya ce za’a samar da Kyamarorin tsaro na “CCTV” a Kano
Gwamnantin jihar Kano da hadin gwiwar wasu kwararru ta sha alwashin samar da Kyamarorin tsaro dake kula da kai komon mutane sama da dubu biyar a fadin jihar.
Mataimakin shugaban shirin Muhammad Bello Dalha ne ya bayyana hakan yayin da yake yiwa manema labarai karin haske kan nasarar da shirin ya samu.
Muhammad Bello Dalha ya kara da cewa matakin ya zama wajibi, don kula da lafiya da dukiyoyin al’ummar Kano, dai-dai lokacin da matsalar tsaro ke ci gaba da ta’azzara a sassa daban-dabam.
Da gaske jami’an tsaro na aiki da “CCTV” a Kano?
Kungiyar dattawan Arewa ta nemi Buhari ya sauya manyan jami’an tsaro
Mataimakin shugaban shirin ya ce Gwamnatin Kano ta maida hankali wajen samar da wadannan na’urorin kyamara, don yin gogayya da sauran kasashen ketare don bunkasa sha’anin tsaro.
Muhammad Bello Dalha ya bukaci al’ummar jihar Kano da su ci gaba da basu hadin gwiwa wajen kula da wadannan na’urori, don samar da ci gaban da ake bukata.
You must be logged in to post a comment Login