Labarai
Ganduje ya haramta amfani da injin Janareto a Kasuwar Sabon Gari
Gwamnatin Jihar Kano ta sanar da haramta amfani da injin janareto a kasuwar Sabon Gari, kasancewar yana daga cikin dalilan da ke haddasa tashin gobara a kasuwar.
Gwamnan Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje ne ya bayyana hakan da yammacin jiya lokacin da ya ziyarci kasuwar ta Sabon gari domin kaddamar da aikin feshin maganin kashe kwayoyin cuta.
Dr Abdullahi Ganduje ya kara da cewa la’akari da hayakin da injin ke fitarwa wanda kuma ke shafar lafiyar al’umma ne ya sa ya zama wajibi a koma kacokan kan amfani da na’ura mai amfani da hasken rana wato solar.
Ba ma bukatar sanya Solar -‘yan kasuwar Sabon gari
Babu hannu na a musgunawa ‘yan kasuwannin Kwari da Sabon Gari – Ganduje
Haka zalika gwamnan ya kuma ce makasudin yin feshin maganin shi ne domin kare yaduwar cutar Corona da ma wasu sauran cututtuka a kasuwar.
Wakiliyarmu Zahra’u Nasir ta rawaito cewa gwamnan ya alkawarta duba yiwuwar karin kwana guda don bude kasuwanni, matukar aka martaba matakan kariya da aka shimfida.
You must be logged in to post a comment Login