Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Manyan Labarai

Ganduje ya jagoranci taron majalisar zartarwa ta jiha a Abuja

Published

on

Gwamnan jihar Kano Dr, Abdullahi Umar Ganduje ya jagoranci zaman majalisar zartawa na jiha a gidan saukar baki na Kano a babban birnin tarayya dake  Abuja.

Gwamnan dai ya jaoranci zaman majalisar zartarwar a Abuja kasancewar a halin yanzu yana gudanar da wasu ayyuka na kasa a can.

Wannan na kunshe cikin sanarwar da mai baiwa gwamnan shawara na musamman kan kafafa sada zumunta Salisu Tanko Yakasai ya fitar a yau Litinin.

Daga cikin wadanda suka halacci taron akwai maitamakin gwamnan Kano Dr, Nasiru Yusuf Gawuna da sakataren gwamnati Alhaji Usman Alhaji da shugabar ma’aikata Hajiya Lawan Ahmed da shugaban ma’aikata na fadar gwamnati Ali Haruna Makoda da kwamshinan yada labarai Muhammad Garba da dai sauran su.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!