Labarai
Ganduje ya kaddamar da aikin gina masallatan Juma’a
Gwamnatin jihar Kano ta kaddamar da ci gaba da ginin wasu masallatan juma’a guda biyu akan kudi naira miliyan sha uku tare da gyaran gadar da ta taso daga Kansakali zuwa Dan-sudu a karamar hukumar Tofa wanda aikin zai lakume sama da naira miliyan dari hudu kafin a kammalashi.
Kwamishinan ayyuka da gidaje Alhaji Idris Garba Unguwar Rimi ne ya kaddamar da gina a garuruwan Ginsawa da ‘Yan Sabo da ke mazabar Yanoko duk a karamar hukumar Tofa.
Alhaji Idiris Unguwar Rimi ya ce, ginin masallatan daya ne daga cikin kudurin gwamnatin na kyautatawa al’ummar karkara da kuma share musu kukan su na rashin masallatai a kusa da su.
A nasa bangaren shugaban karamar hukumar Tofa Alhaji Nafi’u Yarimawa ya alkawarta cewa da zarar an kammala ginin masallatan zai samar da shimfidu da sauran kayan bukata na masallaci.
Da yake wakiltar al’ummar garin na Tofa Malam Sani Abdullahi ya bayyana farin cikin sa bisa amsa kiran su da gwamnatin tayi na samar musu da masallaci tare da gyaran gadar ta su.
Wakilin mu Umar Lawan Tofa ya ruwaito cewa a yayin kaddamar da ginin masallatan an bukaci al’ummar yankunan da su rika kula da su don cin gajiyar su yadda ya kamata.
You must be logged in to post a comment Login