Labaran Kano
Ganduje ya mikawa sabbin sarakunan wasikar shedar nadi
Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje ya mikawa sabbin Sarakunan Kano da Bichi wasikar shedar nadi a yanz- yanzu.
Da fari dai Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje ya mikawa Sarkin Bichi Alhaji Nasiru Ado Bayero wasikar shedar nadi a matsayin sarki mai daraja ta daya.
Bayan mikawa sarkin na Bichi Alhaji Nasiru Ado Bayero ne sai gwamnan ya mikawa na Kano Alhaji Aminu Ado Bayero.
Wakiliyar mu ta Fadar gwamnati Zahra’u Nasir ta rawaito cewa, dakin taro ya cika makil da magoya baya da kuma hakimai.
Da Bayan la’asar din nan ne aka fara bikin bada wasikar shedar danin ga sabbin sarakunan da gwamnatin Kano ta yi.
A dai ranar Litinin 9 ga watan nan da muke ciki gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje ya tsige tsohon sarkin Kano Malam Muhammadu Sanusi na II daga mukamin sarkin Kano bayan da ya kwashe kusan shekaru 6 akan mukamin.
Muna dauke da cikkaken labarin anan gaba kadan.
You must be logged in to post a comment Login