Labaran Kano
Ganduje ya nada mace a matsayin shugabar ma’aikata ta Kano
Gwamnan Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya amince da nadin sabuwar shugabar ma’aikata ta jiha Hajiya Binta Lawan Ahmad.
Kafin nadin nata, Hajiya Binta Lawan Ahmad ita ce babbar sakatariyyar ma’aikatar kasuwanci ta jihar Kano.
Hajiya Binta Lawan Ahmad ta maye gurbin Dakta Kabiru Shehu, bayan cikar shekarun sa na aiki a makwanni baya.
Wannan na kunshe ne cikin wata sanarwa da sakataren yada labaran Gwamnan Kano Abba Anwar ya fitar a yau Juma’a ga manema labarai.
Ganduje ya sanyawa sabuwar gada sunan Sheik Kariballah
Majalisar sarakuna : Ganduje ya bada umarnin da a gyara gidan Shattima
Majalisar Sarakuna : Ganduje ya maida martani kan umarnin kotu
Sanarwar ta kuma ce Gwamnan Kano ya amince da nadin masu bashi da shawara da suka hadar da Ali Baba (A Gama Lafiya) a matsayin mai baiwa Gwamnan Kano shawara akan harkokin addinai, da Mustapha Hamza Buhari a matsayin mai baiwa Gwamnan Kano shawara kan harkokin siyasa.
Haka zalika sanarwar ta ce an kuma nada Hamza Usman Darma a matsayin mai baiwa Gwamna shawara kan abubuwa na musamman, da kuma Tijjani Mailafiya Sanka a matsayin mai baiwa Gwamnan Kano shawara kan harkokin masarautu da kuma Yusuf Aliyu Tumfafi a matsayin mai baiwa shugaban kasa shawara kan harkokin karkara.