Manyan Labarai
Ganduje ya rantsar da kwamishinoni ranar tantancewa
Gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje ya rantsar da sababbin kwamishinonin da ya aike da su majalisar don neman sahalewar su.
A jiya Talata ne dai majalisar dokoki ta Kano ta kammala tantance kunshin sunayen kwamishinoni da gwamnan jihar Kano Dr, Abdullahi Umar Ganduje ya aike wa majalisar a ranar Litinin.
Bayan kammalawa ne kuma ta shiga ganawar sirri yayin da nan take ta amince da sunayen kwamishinonin.
Babban daraktan shigar da kara na gwamnati Barrister Lawan D. Yakasai ne ya fara da rantsar da Barrister Ibrahim Muktar a matsayin kwamishinan shari’a kuma babban Antoni janar sai Musa Iliyasu Kwankwaso da dai sauran su.
An dai gudanar da shahadar rantsuwar ne a rufafen dakin wasa na Sani Abacha dake Kofar Mata da yammacin jiya Talata.
Daga cikin kwamishinonin da aka rantsar akwai tsohon kwamshinan yada labarai Kwamared Muhammad Garba a matsayin sabon kwamishinan yada labarai da Dr, Zara’u Umar Muhammad a matsayin kwamishinan al’amuran mata.
Sauran su ne mataimakin gwamnan jihar Kano Dr, Nasiru Yusuf Gawuna a matsayin kwamishinan ayyukan gona da Murtala Sule Garo a matsayin kwamishinan kananan hukumomi, da Injiniya Mu’azu Magaji a matsayin kwamishinan ayyuka da Musa Iliyasu Kwankwaso a matsayin kwamishinan raya karkara yayin da kuma Dr, Kabiru Ibrahim Getso a matsayin kwamishinan Mahalli.
Daga cikin su akwai Nura Mohammed Dankadai a matsayin kwamshinan kasafi da tsare-tsare sai Shehu Na’Allah Kura a matsayin kwamishinan Kudi da bunkasa tattalin arziki da Dr, Mohammed Tahir Adam a matsayin kwamishinan al’amuran addini.
Haka zalika akwai Dr, Aminu Ibrahim Tsanyawa a matsayin kwamishinan Lafiya da Sadiq Aminu Wali a matsayin kwamishinan albarkatun ruwa da Mohammed Bappa Takai a matsayin kwamishinan kimiyya da Fasaha da Kabiru Ado Lakwaya a matsayin kwamishinan Matasa da wasanni da Dr, Mariya Mahmoud Bunkure a matsayin kwamsihinan raya al’adu da kuma Mukhtar Ishaq Yakasai a matsayin kwamshinan ayyuka na mussaman da Mahmoud Muhammad a matsayin kwamishinan ciniki da masana’antu da Muhammad Sunusi Saidu a matsayin kwamishinan ilimi da Barrister Lawan Abdullahi Musa a matsayin kwamishinan gidaje da sufuri.
Rahotanin sun bayyana cewar, anyi taron majalisar zartarwa ta jiha da misalin karfe tara na daren jiya a fadar gwamnati wanda gwamnan jihar Kano Dr, Abdullahi Umar Ganduje ya jagoranta.