Manyan Labarai
Ganduje ya sabunta yarjejeniyar tallafin karatun Digiri na biyu da kasar Faransa
Gwamnatin Jihar Kano ta bayyana cewa za ta sabunta yarjejeniyar tallafin karatu na tsawon shekaru biyar da kasar Faransa.
Gwamna Dr Abdullahi Umar Ganduje ne ya bayyana hakan yayin ziyarar da ya kai kasar ta Faransa, yana mai cewa, gwamnatin tasa za ta sabunta yarjejeniyar karatu dake tsakanin jihar da gwamnatin kasar, a karkashin yarjejeniyar tallafin karatu ta Kano da Gwamnatin kasar Faransa, ta tsawon shekaru biyar da za ta fara daga badi.
Wannan na kunshe ne cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun sakataren yada labaran gwamnan Abba Anwar ya raba wa manema labarai a jiya Laraba.
Jaridar Solacebase ta ruwaito cewa, gwamnan ya kuma ce, an fara gudanar da tsarin ne tun a shekara 2016.
Gwannan ya ce karin tsawon shekaru biyar din an yi shi ne domin masu karatun digiri na uku su samu isashshen lokacin kammala karatunsu, a matakai daban-daban.
Bayanin ya bayyana cewa yabon kasancewar hadin gwiwar karatu tsakanin jihar Kano da Gwamnatocin Faransa, Abba Anwar ya bayyana cewa “abunda mukeyi a yanzu shine mun tanadi shirye shirye masu ilimantarwa a inda muke tsara shirinmu na karatu.
Misali a wannan shiri, zamuyi amfani da malaman gaba da sakandare, wanda in sunje sun dawo zasu koyawa dalibansu abinda suka je suka koyo kuma suka goge akai.