Connect with us

Coronavirus

Da dumi-dumi : Ganduje ya sanya dokar yin kulle a Kano

Published

on

Gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje ya sanar da rufe jihar na tsahon kwanaki 7 a wani bangare na rage yaduwar Coronavirus a jihar ta Kano.

Bayanin hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da Sakataren yada labaran Gwamnan jihar Kano Malam Abba Anwar ya fitar.

Sanarwar ta kuma ce rufe jihar zai fara aiki ne daga ranar Alhamis 16 ga watan Aprilu zuwa ranar Ashirin da uku ga watan na Afrilu.

Sanarwar ta kara da cewa gwamman na Kano Abdullahi Umar Ganduje ya ce hana shige da ficen zai fara aiki ne daga karfe goma na daren ranar ta Alhamis.

Hakan na zuwa ne dai dai lokacin da aka samu Karin mutum daya dake dauke da cutar inda jumilla suka zama mutane hudu ke dauke da cutar a jihar ta Kano.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 338,464 other subscribers.

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!