Connect with us

Coronavirus

Da dumi-dumi: Gwamnatin Kano ta tabbatar da karin mutum 5 dake da cutar Corona

Published

on

Ma’aikatar lafiya ta jiha ,ta tabbatar da cewar an kara samun mutum biyar da suka kamu da cutar Corona Virus, a Yanzu haka wanda jimilar ta kawo zuwa yanzu mutum Tara ke dauke da cutar a Kano.

Ma’aikatar ta bayyana haka ne ,a shafin ta na Twitter ,in da ta ce zuwa yanzu haka a yau Laraba an samu karin mutum biyar da aka tabbatar sun kamu da cutar.

Jihar Kano, dai na daya daga cikin jihohin da suke fuskantar barazanar yaduwar cutar ,tun bayan da aka samu mutum daya da ya kamu da ita a farkon makon nan, wanda hakan yasa a jiya Gwamnan jiha Abdullahi Umar Ganduje, ya saka dokar hana zirga -zirga a cikin jihar wacce zata fara aiki a gobe Alhamis da karfe 10 na Daren ranar.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 338,760 other subscribers.

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!