Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Coronavirus

Covid-19: Kungiyoyin kishin al’umma su tallafawa mabukata-Hotoron Arewa

Published

on

Kwamitin tallafawa mabukata da marayu na Unguwar Hotoron Arewa, ya bukaci kungiyoyin kishin al’umma na kasashen ketare da na unguwanni da su tallafawa mabukata da kayan abinci da kudin kashewa a wannan lokaci da ake fama da annobar Corona.

Shugaban kwamitin Muntari Garba ne ya bayyana hakan yayin da yake mika tallafin naira dubu biyar ga mabukata dake unguwar ta Hotoron Arewa don rage musu radadin da suke ciki a wannan lokacin da ake zaman gida sanadiyyar annobar Corona.

Ya kuma ce a wannan lokaci al’umma da basu dashi na bukatar taimako musamman na kayan abinci duba da yadda kayayyakin amfanin yau da kullin kara tsada a kasar nan.

Muntari Garba ya ce idan mawadatan dake kasar nan za su himmatu wajen tallafawa wadan da basu dashi ba’za’a tsinci kaiba a halin da ake ciki na babu ba.

Covid-19: Gwamnatin tarayya ta bada umarnin bayar da tallafi ga mabukata

Covid-19: Ganduje zai fara raba tallafin kayan abinci

Ya kuma ce duba da yadda aka aje mutane a gida a wannan lokacin shine ya sanya akayi karo-karo a tsakanin mawadatan dake yankin don tallafawa wadan da basu dashi.

Muntari Garba ya ce za su ci gaba da gudanar da bada tallafin lokaci zuwa lokaci musamman a lokacin Azumin watan Ramadan dana bikin Sallah don sanya walwala a zukatan wadan da basu dashi.

Wasu daga cikin mutanan da aka baiwa tallafin na naira dubu biyar din sun bayyana farin cikin su tare da kiraga sauran al’umma dasu rinka tallafawa wadan da basu dashi.

Kungiyar ta Hotoron Arewa ta tallafawa sama da mabukata 90 da suka fito daga yankin na hotoron Arewa.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!