Connect with us

Coronavirus

Ganduje ya tabbatar da bullar cutar Corona a Kano

Published

on

Gwamnan Jihar Kano Dakta Abdullahiu Umar Ganduje ya tabbatar da samun bullar cutar Corona a nan Kano.

Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana hakan ne lokacin da yake jawabi ga manema labarai dangane da bullar cutar da yammacin yau a nan Kano.

Ya kuma ce wanda ya kamu da cutar tsohon jakadan kasar nan ne a Kasar waje.

Da Dumi-Dumi: An samu bullar Corona Virus a Kano

Ganduje ya kuma sanar da wasu sabbin tsare-tsaren da ya fito da su a nan Kano don ci gaba da yaki da cutar, wadanda suka hadar da hana direbobin adaidaita sahu daukar fasinja sama da daya a cikin baburansu.

Ya kuma ce za’a ci gaba da tattaunawa da malamai da shugabannin kasuwanni da ma sauran masu ruwa da tsaki don ganin an samu nasarar yaki da cutar a nan Kano.

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 338,760 other subscribers.

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!