Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Coronavirus

Ganduje ya gudanar da feshin magani a inda mai dauke da Corona ya ziyarta

Published

on

Gwamnatin jihar Kano ta bada umarnin yin feshi a guraren da ake zargin Wanda ke dauke da cutar corona a nan Kano yayi mu’amala da su a kwanakin nan, a wani mataki na dakile yaduwar kwayar cutar ga al’umma.

Kwamishinan muhalli na jihar Kano Dakta Kabiru Ibrahim Getso ne ya bayyana hakan a yau, yayin gudanar da feshin magani a asibitoci da masallatan da mai dauke da cutar ya ziyarta.

Dakta Kabiru Ibrahim Getso ya ce gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya baiwa ma’aikatar muhalli damar ci gaba da yin feshi a gidajen yari da barikin sojoji da ke ciki da wajen jihar Kano.

Ganduje ya tabbatar da bullar cutar Corona a Kano

Da Dumi-Dumi: An samu bullar Corona Virus a Kano

Farfesa Suwaid Abba Muhammad daya ne daga cikin shugabannin asibitocin da Mara lafiyar ya ziyarta don duba lafiyar sa ya ce zasu dauki matakan da suka kamata dan ganin cutar bata yaduba.

An gudanar da feshin a mallacin Aminuddeen Abubakar da Masallacin Umar Faruk na Dan Adalan Kano da ke unguwar Nassarawa da Kuma wasu Asibitoci masu zaman kan su guda uku wadanda Mai dauke da cutar coronan ya ziyarta don yi masa gwaji.

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!