Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Ganduje ya shiga alhini bisa rasuwar Aminu S. Bono

Published

on

Shugaban Jam’iyyar APC na kasa, Dr Abdullahi Ganduje ya yi alhini bisa rasuwar darakta masana’antar shirya fina-finai ta Kannywood Aminu Surajo Bono.

Hakan na ƙunshe ne ta cikin wata sanarwa da Babban Sakataren yada Labarai na jam’iyyar APC Edwin Olofu, ya fitar yau Talata.

Sanarwar ta ruwaito cewa, Ganduje ya ce, ya kadu matuka bayan samu labarin rasuwar wannan shaharren Mai bayar da umarni kuma jarumi a masana’antar.

Dakta Abdullahi Umar Ganduje, wanda ya ce, rasuwar Darakta Aminu Surajo Bono ba kamaramin rashi ba ne ga masana’antar Kannywood, ya kara da cewa rasuwar daraktan ta bar babban gibi a masana’antar.

Shugaban jam’iyyar ya kara da cewa Darakta Aminu Surajo Bono ya yi amfani da lokacinsa wajen bunkasa masana’antar Kannywood ta hanyar gudanar da tsaftacacciyar rayuwa.

Haka kuma, ya ce, “Na kadu matuka da samun labarin rasuwar Darakta Aminu Surajo Bono, Wannan ba rashi ba ne kawai ga masana’antar Kannywood ba. Babban rashi ne ga al’umma.

“Ina amfani da wannan dama dan mika ta’aziyya ga iyalansa da ‘yan uwansa da masana’antar Kannywood. Ina rokon Allah ya basu juriyar wannan rashi.

“Tabbas Darakta Aminu Surajo Darakta Aminu Surajo a cikin finafinai da kuma zahiri abar yabawa ce.”

Dr Abdullahi Ganduje ya ce ya na rokon Allah SWT da ya bai wa iyalansa da masana’antar kannywood juriyar wannan baban rashi, ya na mai rokon Allah SWT da ya gafarta matawa mamacin.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!