Labaran Kano
Ganduje ya yi kira ga dalibai kan su yi amfani da sana’o’in da suka koya
Gwamnatin jihar Kano ta bukaci sabbin daliban da aka yaye daga kwalejin horas da aikin karafa wato Metallurgical Training Institute dake garin Onitsha wajen yin amfani da abin da suka koya don ciyar da jihar Kano gaba.
Kwamishinan ma’aikatar kimiyya, fasaha da kere-kere na jiha Alhaji Muhammad Baffa Takai ne ya bayyana hakan, yayin tallafawa daliban da Gwamnatin Kano ta dauki nauyin karatun a kwalejin da kayan aiki.
Guda daga cikin iyayen yaran da suka yi kwasa-kwasai daban-dabam na aikin karafa da sauran fasahohi Malam Kabir Usman ya tabbatar da cewa za su nusar da ‘ya’yan su don ganin sun yi amfanin da tallafin don su samu madogara.
Ganduje ya nada sabbin mutum biyu a matsayin masu taimaka masa
2023: Gadar Ganduje a APC Barau ko Gawuna?
Ganduje ya nada mata masu ba shi shawara guda 5
Su ma wasu daga cikin daliban sun bayyana jin dadin su da wannan ni’ima da Allah yayi musu na samun horo kan wadannan kwasa-kwasai, da suka shaida cewar da suyi amfani da ilmin da kuma kayayyakin aikin da aka basu don bada ta su gudunmawar wajen ciyar da al’umma gaba.
Wakilin mu Umar Idris Shuaibu ya ruwaito daliban su takwas sun karbi tallafin kayan aiki da kudi Naira dubu 93 kowannen su.