Labaran Wasanni
Ganduje zai daga likkafar asibitin garin Bichi
Ma’aikatar lafiya ta jihar Kano ta bukaci ‘yan kwangilar da ke aikin gina sabon asibitin garin Bichi da su gaggauta kammalawa cikin kankanin lokaci, kasancewar gwamnatin Kano na kokarin daga linkafar asibitin.
Kwamishinan lafiya na jihar Kano Dakta Aminu Ibrahim Tsanyawa ne ya bayyana hakan lokacin da ya kai ziyarar duba aiki a asibitin na Bichi a yau Laraba, yana mai cewa aikin asibitin kudiri ne na gwamnatin jihar Kano don daga darajar asibitocin masarautun Kano guda hudu.
Dakta Aminu Tsanyawa ya ce tun da fari ‘yan kwangilar sun yi alkawarin kammala aikin kafin karshen shekarar da muke ciki sai dai har yanzu sun gaza kammalawa.
Kwamishinan ya ce gudanar da aikin shi zai bada damar daga likkafar asibitin zuwa babban asibitin kwararru wanda zai kunshi gadajen kwanciya kimanin dari hudu mai bangarori da dama.
Kwamishinan ya yabawa ma’aikatan asibitin bisa yadda suke gudanar da ayyukansu inda ya bukace su da rika amfani da kayan kariya daga cutar corona don kiyaye lafiyar su.
Wakiliyar mu Aisha Shehu Kabara ta ruwaito cewar gwamnatin jihar Kano ta kawo na’urorin zamani da za’a rika duba marasa lafiya a zamanance a asibitocin masarautun jihar guda hudu don inganta lafiyar mutanen karkara.
You must be logged in to post a comment Login