Labaran Kano
Ganduje zai dauki likitoci 44 a dukkanin kananan hukumomi

Gwamnan Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana cewa, jihar za ta dauki likitoci aiki dai-dai daga kananan hukumomi 44 na jihar, don bunkasa yanayin kiwon lafiyar al’umma.
Gwamna Ganduje ya bayyana hakan ne yayin taron lafiya a matakin farko na shekarar 2020 da akayi jiya anan Kano.
Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya ce, a kokarin gwamnatin Kano na bunkasa harkokin kiwon lafiya a matakin farko, Gwamnatin jihar za ta sauya wajen da ma’aikatar hukumar kula da lafiya a matakin farko za su rika karbar albashi daga ma’aikatar kananan hukumomi zuwa hukumar bunkasa lafiya a matakin farko ta jiha.
Yayin da yake bude taron, ministan lafiya Dr. Osagie Emmanuel Ehanire ya ce gwamnatin tarayya na yin hobbasa wajen ganin tsarin lafiya a matsakin farko ya inganta, don su rika yin aiki awa 24 a kullum.