Labarai
Ganduje zai tallafawa kungiyar Akantoci da cibiyar bada horo a Kano
Kungiyar Akantoci ta kasa ta ce, zata yi nazari akan ayyukan ta da nufin kawo gyara don kawo cigaba a kasar nan.
Shugaban kungiyar na kasa Muhammad Mainoma ya bayyana hakan a yau ya yin ziyarar da ya jagoranci ‘ya’yan kungiyar zuwa fadar gwamnatin Kano a yau.
Muhammad Mainoma ya kuma bukaci gwamnatin Kano da ta tallafa musu wajen samar da cibiyar da zata rika horar da Akantoci masu tasowa anan Kano.
Mainoma ya kara da cewa sun zo Kano ne domin gudanar da taron tunatarwa akan ayyukan su, wanda zai mayar da hankali akan abubuwan da suka shafi gwamnatin kwarai da auyukan ta.
Ana sa bangaren gwamna Dr Abdullahi Umar Ganduje ya ce zai duba bukatun su wajen ganin ya taimaka wa kungiyar don samar musu da cibiyar anan Kano.
Wakiliyar mu Zahrau Nasir ta ruwaito cewa gwamna Ganduje ya kuma karbi bakuncin tawagar makarantar koyar da hafsoshin soji ta Jaji a fadar sa.
You must be logged in to post a comment Login