Labarai
Gargadi : ‘Yan Najeriya ku sabunta rajistar asusun ajiyarku a Banki ko a rufesu – Buhari
Gwamnatin tarayya ta bukaci dukkannin masu asusun ajiya na bankuna ko cibiyoyin kudi a kasar nan da su gaggauta zuwa su sabunta rajistar asusun nasu.
Hakan na cikin wani sako ne da gwamnatin tarayya ta wallafa a shafinta na Twitter a jiya alhamis.
Sakon ya kuma ce wannan umarni ya shafi dukkannin masu asusun ajiya a bankuna ko cibiyoyin kudi ko kuma kamfanonin inshora.
Haka zalika sanarwar ta ce, wannan ya shafi duk wani mai ajiya komai yawan asusun ajiyarsa na banki to wajibi ne ya bi kowanne daya bayan daya domin sabunta rajistar.
A cewar gwamnatin tarayya, sabunta rajistar zai taimakawa bankunan da cibiyoyin kudi da su gudanar da ayyukansu kamar yadda ya kamata, wanda kuma hakan ya dace da dokar harajin kudin shiga ta shekarar dubu biyu da goma sha tara.
Bugudakari an karkasa sabunta rajistar gida uku wanda ya hada da masu asusu na kamfanoni da na daidaiku da kuma wadanda ke kula da asusu a madadin wasu.
Sanarwar ta kuma ce duk wanda ya gaza sabunta rajistar za a dauki tsauraran matakai akansa da ya hada da: cin tararsa ko rufewa ko kuma a hanashi damar amfani da asusun ajiyarsa.
You must be logged in to post a comment Login