Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

An fara sauraran karar matasa dake sace-sace a Kano

Published

on

Kotun majistiri dake zamanta a titin Court road karkashin jagorancin mai shari’a Auwalu Yusuf Suleiman ta fara sauraran kara da aka shigar gabanta ana tuhumar wasu matasa da suka addabi al’ummar unguwar Rijiyar Zaki da sace-sace

Tun farko dai an gurfanar da matasan ana zarginsu da yin fashi da makami da kuma kwace jakunan mata da wayoyi.

Bayan mutanen unguwar ta Rijiyar Zaki suka kai korafin su zuwa rundunar ‘yan sanda jihar Kano, sai rundunar ta baza komarta inda ta samu nasarar cafke matasan su biyu masu shekaru goma sha takwas.

Matasan da ake tuhuma sun hada da Abdu Abdullahi da kuma Ibrahim Kabiru inda kuma sauran suka tsere.

Wakilin mu na kotu Bashir Muhammed Inuwa ya ruwaito cewa mai sharia Auwalu Yusuf Suleiman ya tasa keyar su zuwa gidan gyaran hali, inda za
a ci gaba da sauraran karar a ranar ashirin da takwas ga watan gobe na Oktoba.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!