Labaran Kano
Garin da ake aure akan naira dubu hamsin (N50,000) kacal a Kano
Dagacin garin Kera dake karamar hukumar Garko a nan Kano ya sanya dokar kayyade kudin aure da sadaki baki daya akan kudi N137,000 ga budurwa, bazawara kuma N50,000.
Kusan watannin uku kenan da dagacin Mallam Bello Musa ya sanya wannan doka, sai dai wasu daga al’ummar garin sun koka bisa wannan sabon tsari.
A zantawar da Freedom Radio ta yi da wasu iyaye a garin sun bayyana cewa ko kadan ba za su lamunci wannan tsari ba a don haka sun shirya tsaf domin kai kokensu gaban hukumar karbar korafe-korafe ta jihar Kano.
Haka kuma Freedom Radio ta tuntubi dagacin wanda ya bayyana cewa wannan doka fa sun yanketa ne domin samar da masalaha a garin, kuma al’umma da malaman garin duka sun amince da wannan doka.
Idan zaku iya tunawa dai a watan Janairu na shekara ta 2017 mahukunta a karamar hukumar Danbatta dake nan Kano, suma suka kaddamar da dokar kayyade aure sai dai ta samu cikas a karshe.
Rubutu masu nasaba:
Amarya ta haihu bayan wata hudu da Aure
An gurfanar da uba da ‘yarsa gaban kotu bisa zargin shirya auren bogi