Ƙetare
Ghana: Matasa 6 sun rasu 22 sun jikkata a hargitsin da ya faru yayin ɗaukar sabbin sojoji

Mutane shida sun mutu yayin da wasu 22 suka samu raunika sakamakon hargitsin da aka samu a wajen ɗaukar aikin soji a Ghana.
Rundunar sojin kasar ta ce, matasa masu neman aikin ne suka ture shingen jami’an tsaro kuma suka yi tururuwa cikin filin wasa na birnin Accra, inda aka samu asarar rayukan.
Rahotonni sun nuna cewa, rashin aikin yi a ƙasar Ghana mai ɗimbin matasa ya kai kashi 32 cikin ɗari, lamarin da janyo cunkoso a cibiyoyin ɗaukar aiki.
Shugaban Ghana, John Mahama, ya ce gwamnatinsa ta ƙudiri aniyar bai wa dukkan matasan ƙasar damar shiga aikin soja.
Hukumomi sun ci gaba da aikin tantance masu neman shiga sojan bayan ƙura ta lafa, inda suka bayar da tabbacin ɗaukar matakan kariya.
You must be logged in to post a comment Login