Labarai
Gobara ta ƙone ɗakin kwanan ɗaliban makarantar Kwana a Sumaila

Wata gobara ta ƙone ɗakin kwanan ɗalibai mata a makarantar Dano Memorial da ke Gidan Mission a Gani da ke a ƙaramar hukumar Sumaila ta Jihar Kano, amma ba samu rasa rai ko rauni ba.
Jami’in yaɗa labarai na na ƙaramar hukumar ta Sumaila Haruna Gunduwawa, ne ta bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da ya fitar a daren Litinin din makon nan.
Sanarwar ta ce gobarar ta afku ne bayan daliban makarantar sun tafi hutu, inda ta ƙone kayayyakinsu da dama.
Haka kuma sanarwar ta kara da cewa, shugaban ƙaramar hukumar Sumaila, Alhaji Farouk Abdu Sumaila, ya kai ziyara wajen da lamarin ya faru inda ya bayyana alhini tare da ba da gudummawar buhunan siminti 50 domin taimakawa sake gina ɗakin kwanan.
Shugaban makarantar, Rebaran Alhassan Musa, ya gode wa gwamnati bisa taimakon da ta bayar da kuma kulawar da aka nuna musu.


You must be logged in to post a comment Login