Labarai
Gobara ta kone dukiyar Miliyan 15 a rumbun adana kaya a Zamfara

Wata mummunar gobara ta cinye wani babban rumbun adana amfanin gona a yankin Barakallahu da ke garin Gusau jihar Zamfara, inda gobarar ta janyo asara ta sama da Naira miliyan 15.
Hukumar kashe gobara ta jihar Zamafara ta ce sun samu kiran gaggawa tare da isa wurin cikin sauri, amma kayayyakin da ke cikin rumbun—mallakin sun riga sun kone.
Bincike ya nuna sakacin kula da yanayin wutar yankin ne ya haddasa gobarar. Sai dai har kawo yanzu ba a samu rahoton asarar rayuka ko jikkata a yayin gobarar ba.
You must be logged in to post a comment Login