Labarai
Gobara ta tashi a kusa da ma’aikatar lantarki ta ƙasa a Abuja

Gobara ta tashi a kusa da ma’aikatar lantarki ta ƙasa da ke Maitama a birnin tarayya Abuja.
Wannan na cikin sanarwar da Hukumar Agajin Gaggawa ta Najeriya NEMA ta fitar a ranar Talatar makon nan.
Sanarwar ta ce an samu kiran gaggawa da misalin karfe 2 da mintuna 36 na rana, inda NEMA ta hada kai da Hukumar Kashe Gobara ta Tarayya da ta Babban Birnin Abuja tare da tura jami’an ceto zuwa wurin.
Masu bayar da agajin sun yi hadin gwiwa wajen taimakawa aikin kashe gobarar da kuma hana yaduwar ta zuwa gine-ginen da ke kusa, lamarin da ya kai ga shawo kan wutar da misalin karfe 5 da mintuna 45 na yamma.
Hukumar ta ce an kammala aikin bayan an tabbatar da cewa gobarar ba ta kara yaduwa ba.
You must be logged in to post a comment Login