Labarai
Gonaki sama da 10, 000 ne suka lalace a bana – SEMA
Hukumar bada agajin gaggawa ta jihar Kano SEMA ta ce ambaliyar ruwa a shekarar 2020 ta yi sanadiyyar gonaki sama da 10, 000 sakamakon mamakon ruwan sama da aka yi.
Yayin da ambaliyar ta yi sanadiyyar rayukan mutane 56 sai kuma mutane 100 da gini ya faɗo a kansu, da dama kuma suka jikkata.
Shugaban hukumar Kwamared Sale Aliyu Jili ne ya bayyana hakan yayin zantwarsa da Freedom Rediyo.
Jili ya ce, a bana kimanin gidaje 46,000 ne suka lalace sakamakon mamakon ruwan sama da aka samu.
Yana mai cewa an samu ambaliyar ruwa a ƙananan hukumomi 44 na jihar Kano, ba kamar yadda hukumar hasashen masana yanayi ta ce ƙananan hukumomi 23 ba kawai.
Idan dai za a iya tunawa tun kafin saukar damunar a bana, hukumar hasashen masana yanayi ta ƙasa NIMET ta ce “kimanin ƙananan hukumomin jihar Kano 23 za su samu ambaliyar ruwa a shekarar”.
Jili, ya ƙara da cewa, wannan adadi da aka samu na ƙaruwar ambaliyar ruwa ya janyo gwamnati ta gaza wajen magancewa waɗanda ibtila’in ya shafa halin da suke ciki.
You must be logged in to post a comment Login